Za Tunkari ‘Yan Bindiga A Daji Muddun Majalisa Ta Ba Mu IkoA Najeriya yayin da ake ci gaba da jimamin kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa ‘yan banga a jihar Katsina, rundunar mafarauta da kula da tsaron dazuka ta ce ita ma ta rasa jami’anta 81 sanadiyyar ayyukan barayin daji a shekarar da ta gabata.

To sai dai ta yi wa barayin dajin kashedi cewa jami’anta sun shirya tsaf domin sanya kafar wando daya da su.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da salwantar da rayukan jama’ar Najeriya inda ko a kwanannan ‘yan ta’adda sun hallaka ‘yan banga fiye da arba’in a jihar katsina lamarin da ya jefa jama’a cikin alhini.

Shugaban majalisar koli akan lamurran addini musulunci a Najeriya mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na cikin wadanda suka nuna alhini akan wannan rashin.

“ Ya ce zan yi amfani da wannan damar in jajanta wa iyalan ‘yan banga fiye da 40 da ‘yan ta’adda suka hallaka, saboda kawai basu da makamai irin nasu, ba mu son irin hakan ya sake aukuwa, inda wasu zasu rasa rayukansu lokacin da suke aikin kare rayukan wasu jama’a.”

Maharba da Kayan Yakinsu.

Maharba da Kayan Yakinsu.

To sai dai lokacin da ake cikin wannan yanayin rundunar mafarauta da kula da tsaron dazuka ta Najeriya wadda ita ma ta rasa wakilanta 81 sanadiyar ayukkan barayin daji ta gargadi barayin da su shiga taitayin su domin tana dab da sanya kafar wando daya da su.

Babban kumandan rundunar mai fatan zama hukuma bada jimawa ba, Ambassador Osatimehin Joshua Wole, ya ce jami’an sa suna cike da azama ta tabbatar da tsaro a cikin dazuka.

“Yace a shekarar bara ma barayin daji sun kashe mafarauta 81 saboda barayin suna amfani da Muggan makamai, su kuwa baya yuwa su rika irin su saboda har yanzu gwamnatin kasar bata kammala amincewa da su a zaman hukuma ba.

Amma acewar sa alhamdulillah domin yanzu haka kudurin dokar kafa hukumar mafarauta ya tsallake tare da samun amincewar bangarori biyu na majalisar dokokin Najeriya, yanzu sanya hannun shugaban kasa kawai yake jira ya zamo doka.

Saboda haka yace suna gargadin barayin daji da masu satar mutane akan cewa su Sani masu dazuka na asali na dab da zuwa su mallake muhallan su wanda aka sanar musu shekaru aru-aru.”

Dangane da rundunar ta mafarauta kuwa Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar yace duk da yake bai da masaniya akan abubuwan da ke kudurin dokar kafa hukumar su, amma dai kara samun zarata da ke bayar da gudunmuwa ga tsaro ya dace.

“Yace lallai muna bukatar karin masu bayar da gudunmuwa ga samar da tsaro musamman duba da halin da kasarmu take ciki musamman cikin dazuka inda barayin daji suke.

Dama tun lokacin da rashin tsaro ya ta’azzara a Najeriya masana lamurran tsaro ke ta baiwa mahukunta shawarwar akan hanyoyin da suke gani mafita, kamar shawarar samar da zarata da su kula da dazuka, shawarar da Detective Auwal Bala Durumin Iya ya jima yana bbayawa, wadda yace nagge ce dadi goma, domin zata samar da ayukkan yi ga matasa da kuma magance matsalolin rashin tsaro da ake kullawa a dazuka a aiwatar a dazuka kuma a samu maboyar barayin a dazuka.

Yanzu dai amincewa da jami’an kungiyar mafarauta ta zamo cikin hukumomin tsaro kan iya nuna tasirin da zata iya yi wajen samar da tsaro ko akasin haka.

Saurari rahoton Muhammadu Nasir:Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like