Za’a Aurar da mutane 100-Tambuwal


Gwamnatin jahar sakkwato a jiya ne tace za’a Aurar da mutane 100 wata mai zuwa.

A jiya ne komishinan Addini na jahar sakkwato Alhaji Mani katami Ya tabbatar da cewa zasu aurar da mutane guda 100 a jahar sokoto wata mai zuwa.

Katami yace gwamnatin zata kashi kimanin naira miliyan 32 a wannan auren.

Inda yake cewa kowane Ango da Amarya za’a basu Jari yadda zai tallafawa Rayuwarsu.

Kuma za’ayi auren me a bisa yadda Addini ya tanadar a Shari’ar musulunci.

You may also like