Kwamitin da aka kafa domin tsarawa da kuma shirya bikin binne tsohon mataimakin shugaban kasa a zamanin mulkin shagari, Alex Ekwueme ya ce za’a binne tsohon mataimakin shugaban kasar ranar 2 ga watan Faburairu.
Boss Mustafa, sakataren gwamnatin tarayya shine ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi.
Mustafa wanda shine shugaban kwamitin ya samu wakilcin, Ministan Kwadago Chris Ngige wanda shi ma wakili ne a kwamitin.
Kwamitin wanda aka kafa ranar 17 ga watan Disambar 2017 ya fitar da jerin abubuwan da za a gudanar a bikin jana’izar na tsawon kwanaki 9.
Za’a fara gabatar da bikin ne daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa ranar 2 ga watan Faburairu.
Sakataren ya bayyana tsohon zaɓaɓɓen mataimakin shugaban kasar na farko a matsayin wanda ya cimma nasara a bangaren zana taswirar gine-gine, tsara birane, kyautatawa mutane da kuma siyasa.
Mustafa yakara da cewa mutuwar Ekwueme wani rashi ne mai radadi ga iyalansa dama kasa baki daya.