Za’a Ci Gaba Da Bincikar Sarkin KanoBayan saka baki da wasu  tsofaffin Shugabannin kasar nan da wasu masu fada aji su kayi kan majalisar jihar Kano ta janye binciken da takeyi wa masarautar Kano da ya hada da kashe kudaden masarautar da sarki Muhammadu Sanusi II yayi batare da bin ka’ida ba. 


wata sabuwa kuma ta sake bullowa. domin hukumar da ta fara bincike akan hakan ta ce dukda majalisar jihar ta dakatar da binciken ita zata ci gaba.

Hukumar Sauraren Koke-koke ta Jihar Kano ta ce dama can duk takardunta na nan a ajiye saboda haka zata ci gaba da aikin ta,  Domin cewa hukumar ta samu umarnin Kotu data binciki fadar Sarkin har sau biyu.
Wani jami’i a hukumar yace tunda majalisar Kano din ta janye nata binciken akan masarautar Kano su yanzu za su iya komawa su ci gaba daga inda suke tsaya,domin bankado gaskiyar lamari. 
Jami’in yace da ma can ba suji dadi ba da majalisar ta ce itama za ta binciki sarkin kuma hukumar tana da isassun bayanai akan yadda aka kashe kudaden masarautar bayan umarni da ta samu daga kotu har sau biyu ta ci gaba da bincike akan masarautar.
Da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho daga birnin Madina, Shugaban hukumar Muhuyi Magaji yace dukkan bayanan da suka samo  tun farkon binciken na nan a ajiye suke babu abin da ya taba su. 
Yace sauran bayani sai ya dawo daga aikin umrah.
Da muka leka ofishin hukumar, mun tadda ana ta aiki akan wasu takardu da muke ganin suna daga cikin takardun shaidun da hukumar ta samo kan binciken da tayi tun a baya.

You may also like