Za’a Cire Shingayen Karɓar Haraji Na Titunan Ƙasar NanRundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce daga Yau Litinin, jami’anta na musanman za su fara cire duk wani shinge da aka sanya ba bisa ka’ida ba a kan manyan hanyoyin mota a fadin kasar.

Shingayen sun hada da wadanda hukumomin karban haraji ke sanya wa ba bisa ka’ida ba, da na kungiyoyin masu motocin sufuri da na kungiyoyin kwadigo, wadanda suke kawo cikas ga zirga-zirgar jama’a da kaya a fadin kasar.

Cikin wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan ta ce jami’an ta za su kuma kama duk wani mutun ko kungiya da aka samu ta na karbar haraji a hannun masu motoci a kan manyan hanyoyi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce dokar karban kudin haraji a kasar ta haramtawa hukumomi ko wani mutun sanya shinge a kan manyan hanyoyi da nufin karbar haraji.

A cewar rundunar ‘yan sandan, bayanan da ta samu daga korafe-korafen jama’a sun nuna a lokuta da dama, bata gari, na amfani da ire-iren shingayen wajen aikata laifuka, da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami.

You may also like