Za’a Dakatar Da Sanatocin Da Suka Nuna Adawa Kan Canja Ranar zaben Shugaban kasa


Rahotanni daga majalisar tarayya sun yi nuni da cewa majalisar Dattawa na shirin dakatar da sanatocin nan guda tara har na tsawon shekara daya bisa nuna adawa da matakin da majalisar ta dauka na canja ranar zaben Shugaban kasa.

Tun da farko dai, a makon da ya gabata ne, daya daga cikin sanatoci daga jihar Ebonyi, Sanata Ovie Omo-Agege ya nemi afuwar majalisar amma kuma aka ki karbar turbar sa bisa hujjar cewa kalamansu na cewa an canja ranar ce don ganin Buhari bai ci zabe ba, batancin ne ga zauren majalisar.

You may also like