Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Sanata Chris Ngige ya ce nan da dan wani lokaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 29 domin tattaunawa da kungiyoyin kwadago don fitar da tsarin mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan. An tsammanin mafi karancin albashin shine naira dubu hamsin.
Mista Ngige ya kuma ce rahoton da kwamitin sake fasalin mafi karancin albashi na kasa zai bayar za kuma a mika shi ga majalisun tarayya domin dubawa kafin aiwatar da shi.