Za’a Fara Biyan Ma’aikatan Jihar Jigawa Kudin Hutunsu A Cikin Wannan Makon


Gwamnatin Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, Ta Amince A Fara Biyan Ma’aikatan Jihar Jigawa Kudin Hutunsu Daga Yanzu Zuwa Kowanne Irin Lokaci A Cikin Satin Nan Da Muke Ciki Insha Allahu.

Kudin Hutu Wani Kudi Ne Da Ake Biyan Ma’aikata Fiye Da Rabin Albashinsu Duk Shekara, Kyauta. Amma Tsohuwar Gwamnatin PDP Ta Soke Yayin Da Ta Dare Madafin Ikon Mulkin Jihar Jigawa.

Amma Maigirma Gwamna Jihar Jigawa Alh Muhammad Badaru Abubakar, Ya Dawo Da shi, Gwamna Badaru Ya Biya Ma’aikatan Jihar Jigawa Kudin Hutunsu Har Sau Uku Bayan Da ya Dare Karagar Mulkin Kujerar Gwamnan Jihar Jigawa.

Dama Kusan Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Zabi Gwamna Badaru Ne, Bayan Da Ya Yi musu Alkawarin Zai Dawo Musu Da Kudin Hutu Indai Allah Ya kai shi Ga Nasara.

Yanzu Dai A Iya Cewa Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu Ga Ma’aikatan Jihar Jigawa Bayan Da Gwamna Ya Cika Musu Alkwarin Da ya Daukar Musu.

You may also like