Za’a Fara Duban Watan Ramadan Yau Juma’a – SultanMai alfarma Sarkin Musulmai, kuma shugaban majalisar koli ta malamai, NSCIA Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci musulman kasar nan dasu fara neman jinjirin watan Ramadan a ranar Jama’a.
Daraktan sha’anin mulki na NSCIA, Ustaz Isa Christian Okonkwo ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 24 ga watan Mayu, inda ya tayaal’umman musulmai murnan karasowar watan Ramadan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Tun bayan azumin shekarar data gabata, kwamitin neman watan ta shawarci mai alfarma Sarkin Musulmai dangane da ganin wata da a dinga fitar da sanarwar ganin wata a kowanne wata. 

Don haka ne Sultan ya shawarci musulmai dasu fita neman ganin wata a ranar 26 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 29 ga watan Sha’aban.”Inji Ustaz Okonkwo
Sultan yace muddin an ga watan a daren Juma’a, jama’a su taimaka su sanar da sarakunan al’umma, don a sanar da ranar Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan, idan kuma ba’a gani ba, Lahadi 28 ga watan Mayu ya zama daya ga watan Ramadan 1438 bayan hijra.
Daga karshe sanarwar ta kara da shawartan musulmai dasu jajirce wajen ribatan watan Azumin Ramadan, sa’annan majiyar Hausa Online ta ruwaito an bada lambobin wayan daya kamata a tuntuba domin sanar da ganin jinjirin watan kamar haka.
Mallam Hafiz Wali 08036009090
Shaykh Tahir Bauchi 08032103733, 08033058201.
Shaykh Kariballah Kabara 08035537382.
Muhammad Nasir AbdulMuhyi 08065687545, 08024333381.
Shaykh Habeebullahi Adam Abdullahi Al-Ilory 08023126335.
Alhaji Abdul Hamid Oyebode 08037063923
Prof. Z I Oboh Oseni 08033574431.
Shaykh AbdurRahman Ahmad 08023141752.
Malam Simwal Usman Jibrin 08033140010.
Alhaji Yusuf Nwoha 08030966956.
Sheik Bala Lau 08037008805.
Sheik Sani Yahaya Jingir 08065687545.
Sheik Adam Idoko 08036759892.

You may also like