Za’a Fara Karatun Digiri A Gidan Yari a Kano


 

Hukumar Kula Da Gidajen Yari ta Kasa ta bayyana cewa ta na da niyyar gina jami’a a Gidan Yarin Kurmawa da ke jahar Kano domin baiwa fursunoni damar su yi karatun digiri, kamar yadda ake yi a sauran jami’o’i.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano, Alhaji Aliyu Achor a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani biki da aka shirya a gidan yarin.

An yi bikin ne dai domin karrama wani matashi dan shekaru 27 da kayan sana’a da suka hada da keken dinki, da na surfani, da injin yin ziza, bayan da ya kammala zaman gidan yarin na tsawon shekara tara da wata hudu.

Matashin ya samu wannan tagomashi ne a bisa tarbiyya da dattakun da ya nuna yayin da yake zaman kaso.

Babban mai kula da Gidan Yarin na Kurmawa, Alhaji Auwalu Umar Diso ya ce wannan shi ne karo na 20 da hukumar kula da gidajen yari ta ke gudanar da irin wannan biki, inda take zabo wasu da suka kammala zaman su ta basu kyaututtukan da za su taimakawa rayuwarsu.

Da ma dai akwai tsarin koyar da sana’o’i daban-daban a cikin gidan yarin ga fursunoni, kuma a yunkurin hukumar na dorad da wannan karamci ne za ta gina babbar jami’a domin amfanin daurarrun ciki.

You may also like