Gwamnatin lardin Beaucaire ta kasar Faransa ta bayar da umarnin hana sayar da abinci da ba ya dauke da naman alade a kantunan makarantun da ke yankunanta.
Shugaban lardin mai tsattsauran ra’ayi Julien Sanchez ne ya ce, daga ranar 8 ga watan Janairu an daina sayar da abinci mara naman alade a kantunan makarantu wanda aka fara shekaru 40 da suka wuce a matsayin sauyi ga Musulmai, da Yahudawa da ba sa cin alade.
Wannan abu dai ya tunzura iyayen yara inda suka fara shiga kafafan yada labarai suna gabatar da korafinsu.
Iyayen yara sun kafa wata kungiya don ganin yunkurin shugaban bai yi nasara ba.
An samu labaran cewa, iyayen yara sun fara bgudanar da zanga-zanga inda wata daga cikinsu Anne Moiroud ta ce, Ita ba Musulma ba ce, kuma ba wai mai cin ganyayyaki ba ce amma kuma tana nuna goyon baya ne ga iyayen yara da suke zaune a lardin na Beaucaire.
A baya ma a Faransa an taba kawo irin wannan doka a lardin Chalon-sur-Saone inda kotu ta ce hakan ya take hakkokin yara wanda hakan ya sanya ba a yi aiki da tsarin ba.