Za’a Iya Tsige Buhari Idan Ya Matsa Akan Magu – Lauyoyi Manyan Lauyoyin ƙasar  nan suna ta tofa albarkacin bakin su game da batun Sanotoci da su ka ki amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC.

Babban Lauyan nan Mike Ozekhome yace shugaba Buhari bai dace ya kara aika sunan Magu ba don kuwa an yi wannan ba sau daya ba kenan. Ozekome yace kurum sai dai a nemo wani don kuwa ba Magu kadai ne mutum ba.
Shi kuwa Babban Lauya JB Daudu cewa ya yi bai halatta Magu ya kara zama a Ofishin EFCC ba daga yau. Daudu yace kai har ana iya tsige Buhari idan ya kara aikawa Sanatoci sunan Ibrahim Magu. Babban Lauyan yace kwanakin Magu sun kare a matsayin mukaddashi.
Sai dai wasu suna ganin akwai lauje cikin nadi a maganar. Wasu ma dai suna ganin cewa mafi yawan Sanatocin ba za su rasa kashi a duwawun su ba, don haka su ke gudun Ibrahim Magu. Shi dai Ibrahim Magu yace ko ta yaya dai sai ya yaki sata a kasar.
Majalisar Dattawa dai ta ki amincewa ta tantance Magu ne bisa wasu zargi da hukumar DSS ta yi a kansa.

You may also like