Za’a Ladaftar Da Sanatocin Da Suka Nuna Adawa Da Matakin Canja Ranar Zaɓen Shugaban Kasa


Majalisar Dattawa ta nemi kwamitin da’a na majalisar kan ya fara binciken wasu sanatocin da suka fito fili suka nuna adawa da matakin da majalisar ta dauka na canja ranar zaben Shugaban kasa da nufin Ladaftar da su.

Tun da farko ne dai, dan majalisar Dattawa mai wakiltar jihar Delta ta Tsakiya, Sanata Ovie Omo-Agege ya yi ikirarin cewa an canja ranar zaben Shugaban kasar ne don ganin cewa Buhari bai lashe zaben ba wanda a kan haka ne wasu sanatoci suka fice zauren majalisar don nuna adawa da matakin.

You may also like