Za’a Ragewa Jahar Kogi Kujeru Saboda Sun Tura Mace Mai Juna Biyu Aikin HajjiShugaban hukumar jin dadin Alhazai ta kasa wato,NAHCON, Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar Kogi  ta hanyar rage mata kujeru a badi sakamakon barin wata mace mai juna biyu halartar aikin hajjin bana wadda kuma ta haihu a can kasa mai tsarki.

A cewar Shugaban hukumar ta NAHCON, za a kuma d hukunta shugabannin hukumar aikin hajji ta jihar. Alhazan Nigeria Kusan dabu 90 ne ke halartar aikin hajjin bana. Haka kuma alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji. Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna.

You may also like