Za’a Rufe Filin Saukar Jiragen Sama Na Abuja Na Tsawon Wata Shida


FCT International Airport

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rufe filin saukar jiragen sama na Abuja don gyara titin sauka da tashin jirgi ya dace da saukar manyan jirage.

Ministan zirga-zirgar jiragen Hadi Sirika ya ce za a rufe filin jirgin don wannan aiki na tsawon wata 6 inda za a ke amfani da filin saukar jiragen sama na Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya ya zama na wucin gadi.
HaKa zalika ma’aikatar jiragen za ta gyara dakin kashe gobara da sake gina wata sabuwar hasumiyar sadarwa da jirage don dogon gini ya tare hasumiyar da a ke da ita yanzu.

You may also like