Za’a Rufe Kasuwannin Canji Na Bayan Fage A Najeriya Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce za ta rufe illahirin kasuwannin canji na bayan fage domin farfado da darajar takardar kudin kasar wato naira.
Ministar kudi ta kasar Madam Kemin Adeosun ce ta sanar da haka a jiya Talata, inda ta ce tuni aka umarci babban bankin kasar da ya dauki matakan shimfida wani sabon tsari da zai kawo karshen kasuwannin na bayan fage, wadanda ke sayar da dalar Amurka sama da kashi 40 cikin dari fiye da farashin da gwamnati ta kayyade.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ke kokarin durkushe wa sai dai matsalar faduwar darajar naira da kuma yadda ake sayar da dala a kasuwannin bayan fage na kawo tarnaki a kokarin ceto tattalin arzikin.

You may also like