Za’a Sake Sako Yan Matan Chibok


Ministan sadarwa Adebayo Shitu ya bayyana haka yayin taron shekara-shekara karo na uku, na kungiyar al’ummar musulmai dake kudu maso yammacin Najeriya.

Yayin da yayi kira ga yan Najeriya, kan suyi addu’ar samun sauki ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ministan yace gwamnati na aiki tukuru wajen dora kasarnan kan hanyar cigaba. 

Ya kuma kara da cewa a karon farko cikin tarihin kasarnan fannin sadarwa ya samar da kaso 10 na jimillar tattalin arzikin kasa. 

Shitu yace wutar lantarki ta inganta, an samu dai daito a farashin man fetur,raguwar cin hanci da rashawa, da kuma warware rikicin Neja Dalta. 

A nasa jawabin Shugaban kungiyar Sakariyau Babalola,ya shawarci gwamnati da kada tayi kasa a gwiwa a shirin da take na tallafawa talakawa da kuma marasa aikin yi. 

You may also like