Za’a Sasanta Kwankwaso Da GandujeWata babbar kungiyar kiyaye hakkin Bil’adama ta kasa mai suna Rigar Yanci International Foundation ta shirya Kwamitin daidaita rikici tsakanin Tsohon Gwamnan Jihar Kano sanata Rabi’u Musa Kwankaso da Gwamnan Jihar kano mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban kungiyar ta Rigar Yanci Comrade Mustapha Haruna Khalifa ya ce ba zai yiwu manyan yan siyasa irin su Kwankwaso da Ganduje a Jihar Kano’ su dunga jawo rikice-rikice karshe ma har a zubar da jini.

Yace da Kwankwaso da Ganduje cibiyoyi ne na siyasa a Jihar Kano saboda haka rashin daidaito a tsakanin mutanen guda biyu babban kalubale ne a tsakanin Al’ummar Jihar Kano musamman Mata da kananan Yara.

Kowa yaga irin abunda ya faru a tsakanin bangarorin guda biyu a lokacin bikin Sallah (Hawan Daushe), shi yasa kungiyar bazata sake lamutar haka ba.

Shi yasa kungiyar ta kafa Kwamiti domin gayyato mutanen guda biyu domin Samar da matsaya tare da tufke barakar a tsakanin su, domin haka ci gaba ne sosai kuma hakan zai Samar da zaman lafiya a Jihar Kano.

You may also like