Karamin ministan Albarkatun man fetur Dr Emmanuel Ebe Kachikwu ya ce daga watan Janairun shekara mai kama ta 2017 farashin litar man fetur zai sauko kasada N87.
Mista Kachikwu ya bayyana hakane a birnin Port Harcourt. Ya ce tuni har ya amince da sabon tsarin saida man wanda zai fara aiki daga sabuwar shekara.
Minista Kachiku ya ce a karkashin sabon tsarin saida man an cire harajin ba gaira ba dalili da ake karba daga hannun yan kasuwa masu shigo da man fetur din.