Za’a Sha Wahala A Yakin Kwato Birnin Mosul, Inji Obama


Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana cewa yakin kwato birnin Mosul Na Iraki daga hannun ‘yan ta’adda na IS zai yi wahala sosai, duk da yayi amanar cewa za’a murkushe kungiyar.

Mista Obama ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai tare da shugaban gwamnatin Italiya Matteo Renzi a fadar wite house, inda ya kara da cewa za’a yi ta ”kon- gaba -kon baya” a yakin kafin a kai ga yin nasara.

Aman ya ce fara kaddamar da yaki kwato Mosul babban ci gaba ne, kuma zai kai ga kawar da kungiyar ‘yan ta’ddan gabadaya.

haka zalika ya ce ko baya ga yunkurin kawar da kungiyar, gwamnatocin kasashen biyu zasu maida hankali kan tsaro da kuma tallafin jin kai ga fararen hula dake tserewa daga gidajensu saboda yakin da aka yi.

Wadanan kalamen na Obama na zuwa ne a rana ta biyu da dakarun Iraki da mayakan sa kai na Shi’a suka nausa kai Mosul, birni na biyu mafi girma a Iraki a gaggarumin farmakin tsarkake yankin daga duk wata barazanar ‘yan ta’addan IS.

You may also like