Za’a Tsige Abdulmuminu Daga Majalissa Bisa Adawa Da Shugaba Buhari Dubban ‘yan mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano ne suka nesanta kansu daga dan majalisar Wakilan nan da ke wakiltarsu, Hon. Jibril Abdulmumini bisa kiran da ya yiwa Shugaba Buhari kan ya yi murabus.

Da yake ƙarin haske a madadin al’ummar mazaɓar, Alhaji Muntari ya ce sun yanke shawarar dawowa da dan majalisar gida saboda ikirarin da ya yi ya saba ra’ayoyin al’ummar mazabar saboda suna tare da Buhari dari bisa dari.

You may also like