Za’a Yi Amfani Da Akwatin Zaɓe Na Na’ura Wajen Gudanar Da Zaben Kananan hukumomi A Kaduna Gobe


Jihar Kaduna za ta kafa tarihi a gobe Asabar inda za ta gudanar da zaben kananan hukumomi jihar su 23 ta hanyar amfani da akwatin kada kuri’a na na’ura.

Jihar Kaduna ce ta biyu a nahiyar Afrika bayan kasar Namibia da za ta fara amfani da akwatin zamani wanda bayan tantance mai kada kuri’a, zai je kai tsaye ya ga alamomin jam’iyyar a allon akwatin zamani inda zai latsa jam’iyyar da yake ra’ayi.

You may also like