Za’a Zubar Da Jini Idan Har Buhari Ya Kai Ziyara Ebonyi – Kungiyar IPOB Kungiyar nan mai fafitikar kafa kasar Biyafara ta IPOB ta gargadi Shugaba Muhammad Buhari kan cewa idan har ya kuskura ya ziyarci jihar Ebonyi kamar yadda aka tsara a gobe Talata, za a zubar da jini.

Kakakin Kungiyar ta IPOB, Emma Powerful ya jaddada cewa a shirye ‘ya’yan kungiyar suke su sadaukar da rayukansu idan har Buhari ya sa kafa a Ebonyi saboda a cewarsa, Buhari zai ziyarar ce don ya nuna masu cewa mulki na Arewa.

You may also like