Za’ai Jana’izar Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule A Yammacin YauTuni dai gawar marigayi Dr Yusif Maitama sule ta iso garin kano daga garin cairo dake kasar Masar. 

Sanarwar da take fitowa daga fadar sarkin kano, tana cewa za’ai Jana’izar Marigayin a yau da misalin karfe 4 na yamma a fadar sarkin kano dake birnin kano. 

Tuni gwamnatin jihar kano ta sanar da ranar yau a matsayin hutun Jana’izar Marigayi wanda ya kasance babban rashi ga jihar kano dama kasa baki daya. 

Wakilan gwamnatin tarayya suna kan hanyarsu ta zuwa kano a dai dai lokacin hada wannna rahoto inda suka hada da shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, da Sanatocin Kano guda biyu. 

You may also like