Majiyarmu ta rawaito cewa, zaman wanda za a gudanar da shi a ranar Lahadi mai zuwa tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma hukumar ladabtarwa ta MOPPAN, akwai yiwuwar jarumar za ta samu sassauci daga hukuncin da aka yanke mata na kora daga masana’antar.
Hukumar kula da finafinan Hausan dai ta kori jaruma Rahma ne daga masana’antar fim bayan ta kama ta da laifin yin wata wakar bidiyo, inda aka nuno ta hada jiki da wani mawaki mai suna Classiq wanda hakan ya saba dokokin fim din Hausa.