Zababen shugaban Amurka Donald Trump, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasar na 45, inda ya gaji Barack Obama wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 8.
Babban jojin Amurka ne John Roberts, ya rantsar da Mista Trump a bikin da akayi yau Juma’a a birnin Washigton.
Bayan rantsarda dashi, a cikin jawabinsa Mista Trump ya ce “lokacin fada ba cikawa ya wuce, yanzu lokacin aikatawa ne”
Hakazalika a cikin jawabin na sa na farko a matsayin shugaban Amurka, Trump ya ce ”Ba zan kara amincewa da ‘yan siyasa masu fada ba cikawa ba”
Saida alkalin kotun kolin Amurka, Clarence Thomas ya rantsar da Mike Pence a matsayin mataimakin shugaban Amurka, kafin daga bisani a rantsarda Mista Trump.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin hada tsohon shugaba Obama da matarsa Michel, sai kuma ‘yar takara demokrate data sha kayi a zaben Hillary Cliton da mai gidanta tsohon shugaba Bill Cliton da kuma tsohon shugaba George W Bush.