An Zabe Mu ne Domin Muyi Abunda Ba Zai Yiwu Ba – APC


APC-e1472630849635

 

 

A jiya talata Shugaban jam’iyya mai mulki APC reshen kudancin kasarnan, Segun Oni ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun zabe su ne domin su cimma abunda ya ke ba zai yiwu ba.

Jaridar Punch ce ta rahoto shugaban na cewa duk da dai abun da ake so su yi din ba mai yiwu ba ne, za su yi iya kokarinsu. Ya ce yana rokon ‘yan Nijeriya da su yi hakuri kuma su rage nauyin tsammanin da suke wa gwamnati.

Oni ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar ya rigaya ya samu nakasu tun lokacin mulkin PDP kafin ma shugaba Buhari ya hau mukamin.

Ya kuma ce ‘yan Nijeriya su gode Allah cewa APC ce ta samu nasarar zaben bara, kuma ta samu damar sauya akalar kasar daga hanyar hatsari da ta dauka.

Ya ce da PDP ce har yanzu a kan Mulki da abun ba kara lalacewa kawai zai yi ba, da kila yanzu duk mun zama ‘yan gudun hijira.

 

 

cc:alummata

You may also like