Zaben 2019: An Kaddamar Da Gamgamin Yakin Neman Zaben Buhari Na 2019 A Yammacin JiyaYankin kudu maso yammacin Najeriya ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Muhammadu Buhari ta 2019 a karon farko wato Buhari Campaign Organization (BCO) a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari wanda aka kaddamar domin nemar wa shugaba Buhari wa’adi na biyu wanda kuma wa’adinsa na farko zai ƙare a ranar 29 ga Mayu, 2019.

Shugabannin kungiyar BCO daga yankunoni 6 na kasar sun hadu a Abeokuta inda suka kuma gudanar da wani taro wanda zai farfado da kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari a zabe mai zuwa na 2019 a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Shugaban BCO na kwamitin amintattu na Jam’iyyar, Alhaji Kabiru Dutsin-Ma ya ce  sun dauki wannan matakin ne don tabbatar da cewa manufofin Shugaba Muhammadu Buhari sun dore.

Shugaban ya ci gaba da cewa dolene su dauki matakan farfado da kungiyar yanzu domin tabbatar da cewa manufofin shugaba Buhari sun dore da kuma wayar da kan jama’a a kan gagarumin kokari da nasarorin da shugaba Buhari ya yi a gwamnatin sa.

Mambobin BCO na kwamitin amintattu na Jam’iyyar da suka halarci taron sun hada da Hassan Isiyaka (Sarki Kudu), Ambasada (Dr). Abdullahi Bawa Wase da Alhaji Salisu Garba (Sarkin Fulani Sagamu), Cif Otetola Tunde tare da wasu sarakunan gargajiya daga Abeokuta da sauransu.

You may also like