
An kawo karshen bayar da horo na kwanaki hudu a Abuja babban birnin Najeriya ga wasu ‘yan agaji game da irin rawar da za su taka wajen inganta tsaro a wuraren da ke da cinkoson jama’a domin kare rayuwarsu da dukiyoyinsu, musamman ma a lokacin babban zaben kasar da ke tafe.
A watan Fabrairun shekara mai zuwa ne dai ake sa ran gudanar da babban zaɓen a fadin ƙasar.
An horar da ‘yan agaji fiye da 500 ne daga kungiyoyi bakwai na addinin Islama na sassan Najeriya daban-daban.
Daya daga cikin wadanda suka shirya wannan taron horaswan shi ne Abdullahi A. Diggi – babban jami’in bayar da agajin gaggawa a kungiyar Izala ta kasa a Najeriya.
Ya bayyana irin horaswan da aka ba jami’an nasu:
“Ba ma koyar da harbi da bindiga. Muna koyar da samar da tsaro a matsayinmu na ‘yan agaji.”
Abdullahi Ibrahim Ya’u shi ne ya wakilci shi ne wakilin shugaban kungiyar ta Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana wa BBC fatan da suke da shi dangane da shirya wannan horon.
“Aikin ‘yan agaji shi ne kare lafiyar al’umma. Ba a samun nasara sai an yi amfani da bayanan sirri wato intelligence, kuma yanzu kasarmu na fuskantar zabuka nan kusa, kamar yadda Bahaushe ke cewa ‘an kada gangar siyasa’, saboda haka komai na iya faruwa na matsalar tsaro saboda wasu na son cimma burinsu na siyasa”.
Cikin wadanda aka horas akwai Yusuf Muhammad Abba daga garin Kwali na babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Ya ce ganin cewa akwai sassan kungiyar tasu kamar goma a wurin taron horaswar, jami’ai irinsa sun amfana da abubuwan da aka koya musu.
“Gaskiya na ji dadi sosai kuma mun amfana sosai bayan koyon muhimman abubuwan da muka yi.”
Ana dai sa rai cewa irin wannan horon zai taimaka wajen inganta tsaro tsakanin al’umomin Najeriya, ganin cewa ana fuskantar babban zabe a fadin kasar.