ZABEN 2023: Sayen Katin Zabe Ka Iya Zama Illa Ga Arewa
Yankin dai ya damu tare da cewa miliyoyin ‘yan kasar za su rasa ‘yancinsu ta hanyar sayar da katin zabensu ga ‘yan siyasa.

Hakan na zuwa ne bayan sanarwar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC da ke cewa, wasu ‘yan siyasa a kasar na sayan katin zabe na din-din-din daga hannun ‘yan kasa a kudin da bai taka kara ya karya ba. Tuni aka kama wasu mutane biyu tare da yanke musu hukunci bisa laifin mallakar katin zabe ba bisa ka’ida ba a jihohin Sokoto da Kano.

Lamarin da kungiyar dattawan yankin Arewan ta bakin Dakta Hakeem Baba Ahmed, ta ce hatsari ne babba ga yankinsu da ke fama da yawan matsaloli ga kuma yawan al’umma wadanda suka yi rajistar yin zabe.

Sai dai masana na ganin wannan wani salo ne daga wasu jam’iyyun dake ganin ba za su kai labari ba, hakan yasa suke kokarin rage yawan jama’ar da ya kamata su fito kada kuri’a aranar zabe, ta hanyar amfani da talauci da jahilci da ke tura miliyoyin jama’a sayar da yancinsu kamar yadda mai sharhi kan al’amuran siyasa a Najeriya Kabiru Dakata ya bayyana.

Fitattacen Dan siyasa a Najeriya Hon. Saidu kabiru Gombe ya kalubanci ‘yan kasar da su tabbatar da cewa suna karkashin ikon katin zabe da suka mallaka

Ko da yake Hukumar INEC ta jaddada bayyaninta na cewa sayan katin zabe da wasu ‘yan siyasa ke yi ba zai amfane su da komai ba saboda sabuwar na’urar fasahar BVAS da za’a yi amfani da ita a zaben ba zata tantance duk wani da ba a dauki bayaninsa ba tun farko, a cewar Zainab Aminu Abubakar jami’a a sashen yada labarai a hukumar ta INEC

Hukumar INEC dai ta dauki alwashin ganin an hukunta duk wanda aka kama da laifin saye ko sayar da katin zabe, ta na mai gargadin ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa kan cewa, ba za a lamunci duk wani abu da ya sabawa doka ba.

Saurari rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like