ZABEN 2023: Siyasar Jihar Jigawa
Hon. Nasiru Garba Dantiye, wanda ya bibiyi gwagwarmayar neman samar da jihar Jigawa da ma sauran jihohi da aka nema daga tsohuwar jihar Kano, yace babakere da ayyukan ci gaba da gwamnatocin jihar Kano suka yi a cikin kwaryar birnin Kano tare da mayar da yankunan karkara tamkar saniyar ware na daga cikin dalilan da suka sanya mutane a sassan tsohuwar Kano suka rinka kafa kungiyoyin neman a basu jiha domin yankunansu su sami ababen more rayuwa.

Jigawa na daga cikin jihohin da suka sha fama da kalubalen ci gaba a jihohin Najeriya, sai dai a ‘yan shekarun baya-bayan nan ta yi fice wajen karbar bakuncin kungiyoyi da hukumomin ayyukan ci gaba, musamman na ketare irinsu EU, UN, USAID, DFID, da sauransu. Comrade Abdulrazak Alkali, na aiki da wasu daga cikin wadannan cibiyoyi, yace tsare-tsaren kawo sauyin zamani da yawa da wadannan kungiyoyi ke kawowa na samun karbuwa da nasara a jihar Jigawa.

Cikin shekaru fiye da 30 da kirkiro jihar Jigawa gwamnoni 8 ne suka shugabanceta, na soja 4, na farar hula guda 4.

Wasu daga cikin masu kula da lamura na ganin cewa jihar ta Jigawa na fuskantar koma baya ta fuskar hada-hadar tattalin arziki, amma Hon. Nasiru Garba Dantiye, yace la’akari da hada-hadar biliyoyin kudade da ake yi a manyan kasuwannin jihar Jigawa da kuma yadda al’umar jihar suka kware akan harkokin noma na nuna yadda jihar ke da dimbin arziki, sai dai kawai ba a tsara abubuwa a taswirar tafiyar da tattalin arziki na zamani.

Kafin ta koma jam’iyyar hamayya, jam’iyyar PDP ta rike ragamar mulkin jihar tsawon shekaru 8, inda a shekara ta 2015 jam’iyyar APC mai mulki a yanzu ta karbi shugabancin jihar. Kungiyoyin ci gaba na al’uma a sassan jihar na taka rawa wajen tabbatar da shugabanci na gari ga talakawa, inji Comrade Salisu Gumel, daya daga cikin jagororin kungiyoyin ci gaban al’uma.

Duk da cewa Jigawa na cikin jihohin Najeriya da ba a cika samun tashin hankali ba musamman a yayin zabe, al’umar jihar na fatan zabe mai zuwa zai wakana cikin lumana, kuma a sami sahihin sakamako. Galibinsu dai sun yarda cewa, muddin dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar zabe zasu taka rawarsu yadda ya kamata bayan talakawa sun yi zabe bisa cancanta, babu shakka za a samu sakamakon da zai karbu ga kowa da kowa.

Manyan ‘yan takarar da ke neman kujerar gwamnan jihar sun hada da Mustafa Sule Lamido na Jam’iyyar PDP, da Malam Umar Namadi na Jam’iyyar APC, da kuma Malam Aminu Ibrahim Ringim na Jam’iyyar NNPP. Sai dai al’umar jihar Jigawa na bayyana wasu abubuwa da suke muradin gani bayan kafa sabuwar gwamnati. Yayin da wasu daga cikinsu ke ganin ya kamata sabuwar gwamnati ta maida hankali kan bunkasa harkokin noma, ilimi, kiwon lafiya, da dakile matsalar da ke kawo ambaliyar ruwa, da sauran muhimman al’amura, wasu kuwa na ganin akwai bukatar sabuwar gwamnati ta karkata akalarta ga raya birnin Dutse domin ya dace da dukkanin birane a duniya.

Kamar sauran jihohin Najeriya a ranar 11 ga watan Maris ne za a yi zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar Jigawa mai kananan hukumomi 27, kamar yadda yake kunshe a jadawalin hukumar zaben kasar.

Saurari rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like