
Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso, dan siyasa mai shekara 66 ne da ke takarar neman zama shugaban Najeriya na gaba. Ba kasafai akan gan shi babu jar hula a kansa ba. Wannan hula alama ce ta kudurinsa da kuma abubuan da ya cimma a rayuarsa ta siyasa – ya kasance tsohon ministan tsaro, kuma ya rike mukaman sanata da na gwamnan jihar kano har sau biyu.
Mabiyansa na rika sanya wadannan jajayen hulunan, musamman a Kano, inda suka kasance cikin wata kungiyarsa mai suna Kwankwasiyya.
Wannan kungiyar ta rika binsa har zuwa wasu jam’iyyun da ya koma – misali komawarsa jam’iyyar APC daga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar a 2013.
Cikin rayuwarsa ta siyasa, Kwankwaso ya shiga jam’iyyu biyar, kuma a yanzu shi ne dan takarar mukamin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP (New Nigeria People’s Party), wadda ba a san ta ba sai bayan da ya koma cikinta a bara.
Masu nazarin siyasa na cewa da wuya ya iya lashe zaben shugaban kasa kai tsaye, ganin cea yawancin masu goyon bayan nasa na arewacin kasar ne, sai dai zai iya zama karfen kafa ta hanyar hana manyan ‘yan takara biyu – Bola Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Kafin dan takara ya lashe zabe a Najeriya, tilas ya sami kashi 25 cikin 100 na kui’un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin Najeriya 36 baya ga samun kuri’u mafi yawa a zaben.
Chisom Ugbariwould mai nazarin siyasa a najeriya ne, ya shaida wa BBC cewa Kwankwaso na bukatar goyon bayan ‘yan yankin kudancin kasar idan yana son samun nasara.
Wasu sun yi kokarin janyo hankalin Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi, dan takarar jam’iyyar Labour wanda da asali yankin kudu maso gabashin kasar ne.
Wasu na ganin irin wannan hadin kan na iya ba su damar kwace mulki daga jam’iyya mai mulki ta APC.
Sai dai a wata ganawa da BBC, Kwankwaso ya fito karara ya yi watsi da aukuwar wannan al’amarin. Ya ce Peter Obi bai goge a siyasa ba: “Ba za a aiya hada shi da ni ba, domin na shafe shekaru ina yin siyasa.”
Ci gaba a fannin Ilimi
Amma wani dan Kwankwasiyyar mai suna Ibrahim Sharada, wanda kuma dan jam’iyyar NNPP ne, na ganin farin cikin dan takarar nasu “ya zarce yankin arewaci Najeriya.”
Kuma babu shakka idan aka tafi zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, Kwankwaso na iya zama wanda manyan ‘yan takara biyu za su yi zawarcinsa, ganin yadda yake da mabiya sosai a Kano, jihar da ya rike mukamin gwamna a 1999.
Wannan ce shekarar da mulkin farar hula ya kawo karshe – kuma bai fara sanya jar hula ba a wancan zamanin.
Sai bayan shekara goma ya fara sanya jar hula. A takaice ma ya fadi zaben 2003, lokacin da tsohon Shugaba Obasanjo ya nada shi ministan tsaro.
Magoya bayan Rabiu Kwankwaso na sanya jajayen huluna
Ya rike mukamin har zuwa 2007, lokacin da babu matsalar tsaro sosai a Najeriya. Sai dai daya daga cikin manyan manufofinsa shi ne magance matsalar tsaro da ya addabi Najeriya – ta hanyar bunkasa yawan sojojin kasar zuwa mutum miliyan daya ta hanyar dakar karin sojoji 750,000.
Bayan ya sauka daga wannan mukamin sai ya koma siyasar jiharsa, wanda shi ne lokacin da ya kafa kungiyarsa ta Kwankwasiyya, wadda ya samo karfin gwiwar yin haka daga siyasar marigayi Malam Aminu Kano, wanda ya kasance dan siyasan da ake matukar ganin kimar sa domin rawar da ya taka ta kawo sauyi ga rayukan talakawan arewacin Najeriya bayan samu ‘yancin kan kasar.
Rabiu Musa kwankwaso ya ce kungiyarsa ta Kwankwasiyya ta kunshi dukkan manufofin siyasar Malam Aminu Kano – matakin da ya sa ta yi farin jini musamman ga matasan arewacin kasar – wadanda suka rungumi salon sanya jar hula kamar mai gidan nasu.
Wannan kungiyar ta taimaka masa sake lashe zaben gwamna, inda Kwankwaso ya ce a wannan karon ya sami damar biyan muradun kungiyarsa musamman ta hanyar samar da ilimi kyauta a dukkan matakai har zuwa wannan lokacin.
Sai dai ‘yan jihar Kano ne kawai suke cin gajiyar wannan shirin, kuma dalibai na bukatar nuna takardar shaidar cewa su ‘yan asalin jihar ne gabanin su sami cancanta.
Asalin hoton, AFP
Ykwankwaso ya kaddamar da tsarin ilimi kyauta a makarantun firamare da na sakandare
“Ya kaddamar da tsarin ilimi kyauta bayan da ya zama gwamna kuma yana cikin gwamnonin Najeriya da suka kaddamar da tsarin ciyar da dalibai abinci kyauta,” inji dan jarida Yinusa Ahmad a wata hira da yayi da BBC.
Kwankwaso kansa ya kasance mai kokari ne a yayin da yake dan makaranta, inda ya karanta ilimim injiniyar ruwa a matakin digirin da ya samu a Birtaniya da Indiya.
Tuhume-tuhumen badakkalar kudi fansho
Kamar yawancin ‘yan siyasar Najeriya, Kwankwaso ma an tuhume shi da laifukan cin hanci da rashawa.
A 2021, shekara biyu bayan ya sauka daga mukamin sanata, hukumar EFCC ta tuhume shi kan wasu kudaden fansho da aka karkatar da su yayin da yake gwamna.
Ya musanta tuhumar, kuma ya ce bita-da-kullin siyasa ce kawai.
Asalin hoton, KHALEEL NASIR
Kwankwaso na da iyali – yana da mata da ‘ya’ya shida – kuma mutum ne da ke bayyana karfin gwiwa a siyasance.
Ya kasance mutumin da ke son tunkarar duk wata matsala da zummar ganin bayanta, kuma a kullum yana son bayyana abubuwan da yayi, kuma ana iya ganin alamun su a fadin birnin Kano.
A misali dukkan gine-ginen da yayi yayin da yake rike da mukamin gwamna an rubuta sunan “Kwankwasiyya” a jikinsu da manyan bakake baro-baro a rufinsu. Ba ya son kowa yayi saurin mantawa da shi.