Zaben Amurka 2016: Donald Trump Ya Lashe Zaben Amurka



> Trump ya lashe zaben manyan jihohi

……………………
Donald Trump ya lashe manyan jihohi irin su Florida, Ohio, Iowa da kuma North Carolina.  Haka kuma ya lashe Utah, Alabama, Kentucky, South Carolina, Nebraska, Indiana, West Virginia, Mississippi, Tennessee, Oklahoma da kuma Texas, kamar yadda gidan talabijin na ABC ya yi hasashe. Trump ya kuma ci zaben Georgia, Missouri, Montana, Louisiana, Arkansas, Kansas, North Dakota, South Dakota, Idaho da Wyoming – dukkan su jihohi ne na masu ra’ayin rikau.
> George W Bush bai yi zaben shugaban kasa ba

………………………
Tsohon shugaban Amurka, George W Bush, wanda dan jam’iyyar Republican ne, bai zabi Donald Trump da Hillary Clinton ba. Mai magana da yawunsa ya ce bai zabi kowa ba a bangaren shugaban kasa, amma a bangaren ‘yan majalisar dokoki ya zabi jam’iyyar Republican.  Babu wani daga cikin iyalan Bush da ya yi wa Mr Trump yakin neman zabe ko kuma zabensa.
> Clinton ta lashe Nevada

……………………….

Hillary Clinton ta lashe kuri’un jihar Nevada, wacce jam’iyyar Republican ke lashewa a tarihi, sai dai yanzu lamarin ya sauya saboda karuwar al’ummar Latin masu amfani da harshen Spaniya.
> Darajar Dala ta fadi

……………………

Darajar Dalar Amurka da kudin peso na kasar Mexico ta fadi yayin da kasuwar shunku ta Dow ta yi asarar maki 650. Lashe zaben da Mr Trump ya yi  a Ohio babban tagomashi ne a gare shi domin kuwa babu wani dan takarar jam’iyyar Republican da ya zama shugaban Amurka ba tare da lashe zaben jihar ba. Ya kuma lashe zaben Iowa, wacce rabonta da zaben dan jam’iyyar Republican tun shekarar 2004.
> Magoya bayan Clinton na kuka

………………….

Magoya bayan Clinton na cikin rudani ganin yadda sakamakon zaben ke fitowa.
> Babbar nasara ga Amurka – mashawarcin Trump

………………..

Wani babban mashawarci ga Donald Trump, Curtis Ellis, ya shaida wa BBC cewa “Wannan abin alfahari ne. Dare ne mai muhimmanci ga Amurka  da sauran al’ummar duniya.”
> Georgia ta zabi Trump

………………………

Al’ummar jihar Georgia sun zabi Donald Trump da jam’iyyar Republican.  Tun shekarar 1996 suke zabar jam’iyyar, amma Mista Trump zai yi murna domin ganin cewa kuri’un jam’iyyar sun dan ragu a shekarun baya-bayan nan.

You may also like