Sakamakon zaben jihar Ondo da ke kudancin Najeriya da hukumar zaben INEC ta fitar ya zuwa yanzu ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ce a kan gaba.
Zuwa yanzu, INEC ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi 12 cikin 18, abin da ya nuna cewa APC ta lashe zaben kananan hukumomi tara yayin da PDP ta yi nasara a kananan hukumomi uku.
Gwamna Rotimi Akeredolu shi ne kan gaba a zaben yayin da dan takarar jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede yake biye da shi.
Kananan Hukumomi:
Akoko North-West – APC: 15, 809 – PDP: 10,320
Akoko North-East – APC: 16,572 – PDP: 8,380
Akoko South-East – APC: 9,419 – PDP: 4,003
Akoko South-West – APC: 21,232 – PDP: 15,055
Ifedore – PDP: 11,852 – APC:9,350
Akure North – PDP: 12,263 – APC: 9,546
Ile-Oluji/Okeigbo – APC: 13,278 – PDP: 9,231
Akure South – PDP: 47,627 – APC: 17,277
Owo – APC: 35,957 – PDP: 5,311
Idanre – APC: 11,286 – PDP: 7,499
Ondo East – APC: 6,485 – PDP: 4,049
Irele – APC: 12,643 – ZLP: 5,904