Zaben Kungiyar Mahauta Ya Jawo Karancin Nama A Yola​Da yawa daga cikin gidajen da suke Yola Babban birnin jihar Adamawa sun fuskanci karancin nama a kwanakin karshen makon nan, sakamakon kauracewa mayanka da mahautan jihar sukayi domin halartar wurin zaben shugabanninsu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa mahautan sun bar mayankar inda suka dunguma zuwa Lamido Sinima wurin da aka gudanar da zaben. 

Daya daga cikin mahautan Ali Musa, ya fadawa NAN cewa mahautan  sun bawa zaben muhimanci sosai,shine dalilin da yasa suka jingine aiki na rana daya. 

Musa yace sun sanar da manyan abokanan hurdarsu musamman masu gidajen abinci cewa baza a gudanar da aiki ba a ranar. 

Mazauna garin da suka fita siyan nama a wurare daban-daban dake cikin birnin sun koma gida gwiwarsu a sanyaye.

“Nayi mamaki matuka da abinda yake faruwa, naje wurare da dama amma babu nama, kafin daga karshe wani mutum ya fada min cewa babu nama ga baki daya a gari saboda zaben kungiyar mahauta da akeyi.” a tabakin wani ma’aikacin gwamnati mai suna Hussaini Umar.

Wasu daga cikin mahautan da suke da naman da ya kwana a na’urar sanyaya kayayyaki sunyi amfani da wannan damar domin samun riba mai yawa. 

Karancin naman ya kuma shafi masu tsire da yawa dake garin. 

You may also like