- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Twitter,

Asalin hoton, Others
“Zuciyata na ƙuna, ina tunanin yaushe zan sake ganin farin ciki a rayuwata, mutuwar mahaifina ita ce ta fi ɗaga mun hankali, ga shi na rasa komai a rayuwa”, kalmomin Mu’azu Kabir Baso da harin ‘yan bindiga ya tarwatsa danginsa da raba su da muhallansu kenan.
Mu’azu Kabir Baso matashi ne kuma magidanci mai shekara 28 a duniya, da a kullum ya ke zub da hawaye duk lokacin da ya tuna yanayi na uƙubu da ya tsinci kansa sakamakon matsalolin tsaro a Najeriya.
Mu’azu wanda asalinsa ɗan jihar Katsina ne, ya ce ya rasa mahaifinsa da ‘yan uwa a wani ƙazamin hari da aka kai wa gidansu a karamar hukumar Sabuwa ta Katsina.
Mutumin, magidanci ne mai yara biyu, kuma ya shaida mana irin asarar da ya tafka a cikin lokaci kalilan na rayuwarsa, da kuma wahalhalun rayuwa da sabbin nauye-nauyen da ya faɗa a kansa.
Mutumin, ya aiko da labarinsa ne a cikin jerin labaran da BBC Hausa take samu daga ƴan ƙasar, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023.
‘Rashin da ba zan taɓa mantawa ba’
Mu’azu a wata zantawa da BBC bayan karbar labarinsa, ya ce “na rasa iyayena, na rasa muhallina, na rasa ƴan-uwana, rayuwata ta samu karayar arziki ta fannoni daban-daban kama daga ilimi, kiwo da noma da sauran abubuwa rayuwa na yau da kullum.”
Ya ce da sanyin wata safiya aka kai musu harin ba zata, duk da cewa ya tsallake rijiya da baya ba zai taɓa mantawa da kisan mahaifinsa ba, da lalata musu gida da kwashe musu dukiyoyi.
Matashin ya ce a wannan lokaci yana zaune tare da iyayensa kuma ya gama digiri na farko, yana shirin digiri na biyu. Sai dai yanzu wannan buri ya rushe saboda nauyin da ya hau kansa.
“Ba zan taba mantawa da ranar ba saboda mako guda baya kafin harin na karbo shaidar digiri ɗina na nuna wa mahaifina, ya sanya mun albarka da murna, ban yi tunanin zan rasa shi ba nan kusa.”
“Tun bayan mutuwar mahaifina muka shiga uƙuba, saboda mun rasa dan abin da muke tattalin rayuwa da shi.
“Na shiga yanayi mai muni tun bayan wannan lokaci, saboda nauyi ya dawo kai na, matsalar tsaro ta daidaita rayuwata.
“An raba ni da inda na sani na sauya matsuguni na soma wata sabuwar rayuwa, gashi babu abin hannu.”
‘Girman matsin tattalin arzikina’
“Abin sai dai godiya ga Allah, saboda a halin yanzu na gama aikin yi wa kasa hidima, ina ta neman aiki amma ya gaggara,” in ji Mu’azu.
Kamar yadda bayanai ke nunawa, rashin tsaro ya gurgunta fannoni da dama a Najeriya ciki har da na kasuwanci.
Shi ma Mu’azu lamarin rashin tsaron ya taɓa harkokokin kasuwancinsa, ta yadda ba ya tafiya yadda ya kamata.
“A kullum na zauna idan na tuna yadda rayuwata cikin kankanin lokaci ta sauya, kawai sai na shiga hawaye ina tunani anya wannan gwamnati na da tausayi kuwa.
Ina ganin kamar gwamnatin nan ba ta damu da mu ba, saboda ba a wani waiwayen ire-irenmu da harin ‘yan bindiga ya tilastawa hijira.
“Babu wani tsari na taimako ko kai mana agaji ko tallafa mana da ake yi.
“A halin da muke ciki yanzu kusan ina iya cewa babu wani bambanci fa tsakanin wanda ya yi karatu da wanda bai yi ba.
Wannan kaɗan ne daga cikin cikas da matsalar tsaro ta kawo ma rayuwata a matsayina na ɗan kasa na gari.”
‘Na fida rai ga batun siyasa’
Hali na akuba da matsin rayuwa da matsalolin tsaro suka je fa Mu’azu Kabir Baso, sun sa a yanzu yana cewa bai dogara da wani ɗan siyasa ko gwamnati ba.
“Ni gaskiya a wannan lokaci jan hankalin ‘yan uwana matasa nake yi, su nemi hanyoyin dogaro da kai na halali su fita batun ƴan siyasa.
“Na fitar da rai ga batun ‘yan siyasar kasar nan, ni yanzu mafita da rokon Allah nake yi, na ganin sauyi a rayuwa.
“Sai dai duk da hakan ina fatan gwamnati gaba ta kawo mana sauki, ni ba ni da wani zabi ko ra’ayi kan wani ɗan takarar, domin ni kawai kallon guda nake musu.
“Amma duk abin da aka ce Allah, ba a fitar da tsanmani shiyasa nake yi wa ‘yan Najeriya fata nagari.”
Mu’azu ya ce a yanzu haka ya koma zaman Kaduna tare da iyalinsa da wasu ‘yan uwansa domin laluben sabuwar rayuwa.