
Asalin hoton, others
Al’ummar garin Kalmalo a yankin ƙaramar hukumar Illela a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kafa wani kwamiti domin magance matsalar tsaro a garinsu.
Al’ummar garin sun ce kasancewar batun samar da tsaro yana nema ya yi wa gwamnati yawa sakamakon yawaitar tashe-tashen hankulan da wasu yankunan ƙasar ke fuskanta.
Wannan ne dalilin da ya sa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kafa kwamitin inda masu kuɗi da masu mulki da manoma da ‘yan kasuwa da talakawa suka haɗa kai wajen samar da wannan kwamiti.
Wani mazaunin garin mai suna Safiyanu Abubakar ya ce kwamitin na aiki ”ba dare da rana wajen tabbatar da tsaro a garinmu, domin ana gadi, ana kula da shige-da-ficen jama’a a faɗin garinmu”.
Ya ci gaba da cewa ”da zarar sun ga wata baƙuwar fuska da ba su yadda da ita ba to za a tsaya a yi bincike a tabbatar da cewa baƙon alkairi ne ko na sharri, idan ba a yadda da shi ba za a hannunta shi ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakan da suka dace a kansa”.
Al’ummar yankin sun ce suna alfahari da wannan kwamiti sakamkon aikin samar da tsaro ga ilahirin garin.
‘Kwamiti ne mai ƙarfi’
Safiyanu Abubakar ya shaida wa BBC cewa kwamitin nasu mai ƙarfi ne da ya ƙunshi manya da matasa da dattijan gari, kuma suna da dokoki masu ƙarfi na ladabtarwa da tara kuɗi.
”Idan aka saka ka aikin gadi, kuma ka ƙi fitowa to akwai wurin da za a kaika domin ladabtar da kai, kuma dolenka ka bi wannan umarni da aka baka”, in ji Safiyanu
Ya ce akwai kayan sarki da suke sakawa a duk lokacin da suke bakin aiki ta yadda za a gane su a kuma bambanta su da sauran al’uma, kuma akwai hanyar da suke bi wajen tara kudin da suka buƙata domin gudsnar da ayyukansu.
Haka kuma mutanen garin sun yi kira ga sauran al’umomin ƙasar waɗanda ke fama da tashe-tashen hankula da su ɗauki irin wannan dabara tasu domin kuwa a cewarsu matsaloli sun yi wa gwamnati yawa.
‘Muna da na’urar oba-oba domin kiran gaggawa’
Safiyanu ya ce ya zuwa yanzu kwamitin nasu ya samu akalla shekara biyu zuwa uku da kafuwa, ya ce idan lokacin damina ya tunkaro akan sayo rigunan ruwa a raba wa masu gadin.
Sannan kuma da hanyar da suke bi wajen rarraba aikin kwamitin ta yadda wasu suna aikin rana wasu za su yi na dare , sannan akwai ranakun da ake ware wa mutane domin su samu hutu.
Ya ce akwai wani mutum mai hali a garin da ya taimaka wa kwamitin da na’urar kiran waya ta Obo-Oba domin kiran gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.
Haka kuma ya ce suna da kyakkyawar alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu da jami’an tsaro.
”Ai dole idan za ka yi aiki irin wanna kana buƙatar haɗin kan jami’an tsaro kuma a duk lokacin da wani abu ya faru mukan yi gaggawar sanar da su domin su kawo mana ɗauki idan ya fi ƙarfinmu”, in ji shi.
‘Mun haɗa kai a garinmu’
Al’ummar garin sun haɗa kai sosai manya da matasa ta hanyar wannan kwamiti, domin kuwa duk wanda ke cikin kwamitin yana aiki tare da sauran abokan aikinsa, tamkar ‘yan uwansa, a cewar Safiyanu wanda mamba ne a cikin kwamitin.
Ya kuma ƙara da cewa ”Alhamdulillah a wannan gari namu akwai fahimtar juna da haɗin kai tsakaninmu, domin kuwa ko da buƙatar kuɗi ce ta taso, cikin hanzari za a haɗa kuɗin”.
Ya ce ‘yan garin da ke zaune a wasu wuraren na daban, suma sukan bayar da tasu gudunmowar ta hanyar aiko da kuɗi idan ana buƙata domin tallafa wa kwamitin.
Daga ƙarshe kuma ya yi kira ga sauran al’umar da yankunansu ke fuskantar barazanar tsaro da su yi koyi da irin wannan yanƙuri nasu domin kawo wa kansu mafita, kasancewar abubuwa sun yi wa gwamnati yawa a cewarsa.