Zaftare albashi ya haifar da zanga-zanga a Kano


 

 

Dubban ‘yan kwadago ne a jihar Kano suka yi dafifi a bakin hukumar lura da asibitocin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya tare da garkame kofofin ma’aikatun lafiya dan nuna fushi ga mahukunta.

1. Mai in Nigeria (DW)Dubban ‘yan kwadago ne suka fita dan nuna fushi ga mahukunta a Kano saboda albashi

‘Yan kwadagon da suka yi cincirindo a harabar ma’aikatar lafiya ta jihar Kano wadanda a ranar Juma’a suka yi sammako tare da garkame ilahirin kofofin ma’aikatar da ma kofar shiga hukumar asibitocin jihar Kano ba shiga ba fita wai an bawa mahaukaci gadi, rike da takardu da ke nuna adawa da matakin gwamnati na rage albashin ma’aikatan da ke aiki a asibitocin, ‘yan kwadagon sun yi ta rera wakokin yin tutsu ga matakin da suka ce tamkar kisan kai ne ga ‘yan uwansu ma’aikata.

Kabiru Ado Minjibir shi ne shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano, kuma shi ne ya jagoranci wannan gangami ya bayyana cewar suna taya ‘yan uwa jimami ne kasancewar an fara bikin ranar kyautata aiki ta duniya.

Nigeria Kano Laura Stachel Unterricht (WeCareSolar)Albashi mai kyau na bada karfin gwiwa ga aikin na lafiya a Kano

Ya ce bayan sun rufe wasu kamfanoni masu zaman kansu, a bangaren gwamnati ma sun dauki wananan mataki ne bisa matakin rage albashin ma’aikata da gwamnati ta kudiri aniyar yi, kuma matukar ba a cimma sulhu tsakanin wadannan ma’aikata da gwamnati ba, matakin da za su dauka anan gaba zai bayar da mamaki.

Zuwa yanzu dai ma’aikata da dama a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano na kukan cewar rayuwarsu ta shiga halin gigita kasancewar wannan mataki na gwamnati na barazana ga rabin albashinsu, har ma guda daga ma aikatan ke rokon gwamnati ta sake duba maganar duba da yadda kayan masarufi suka yi tsada.

Duk wani kokari na ji daga bakin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano abin ya ci tura, kasancewar sun ce ba za su ce komai ba saboda wannan magana na gaban kotu.

You may also like