zaizayar kasa na kawo barazana ga wasu makabartu dake Kano


Ali makoda kwamishinan muhalli na jihar Kano, ya ce zaizayar kasa ta lalata kaburbura 200 a makabartar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa a jihar.

Kwamishinan ya bayyana haka a jiya Asabar lokacin da ya ziyarci makabartar Tarauni a wani  bangare na bikin ranar tsaftar  muhallin karshen wata.
“Lokacin da muka samu labarin mun ɗauki matakin gaggawa dan ganin cewa matsalar ba ta cigaba ba,” ya ce.

” A yanzu haka mun fara gyaran yawancin makabartun dake jihar musamman wadanda da suke guraren da suke fuskantar barazanar zaizayar kasa.”

Kwamishinan ya yabawa kungiyar cigaban yankin kan yadda take kokarin tabbatar da makabartar ta kasance cikin tsafta.

Yayi alƙawarin cigaba da tallafawa kungiyar musamman ta bangaren samar musu da kayan aiki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like