Zalunci da Cin Zarafin Da Jami’an Sibil Difens Suka Yi Wa Wani Mutum


nscdc-officials

 

An zargi jami’an Sibil Difens a jahar Gombe ta keta haddin wani mutum, inda suka yi masa duka, suka aske masa kai sannan suka cusa gashin a bakinsa, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bayyana.

Dan kasuwan mai suna Abdullahi Ibrahim ya bayyanawa jaridar Premium Times cewa ya fuskanci cin zarafin ne a sakamakon kafewa da ya yi na kin sauya wata cazar waya da wani jami’in sibil Difens din ya saya, ya kuma dawo masa da ita cewa ta baci.

Ibrahim ya bayyana cewa yaronsa ne ya sayarwa Bala Yayari, Mataimakin Sufritendan sibil Difense a jahar Gombe caza akan naira 1500, kuma sai da aka gwada cazar ta na yi.

 

Sai dai ya bayyana cewa jami’in ya dawo da cazar shagon da ke kasuwar Arawa a jahar ta Gombe daga bisani ya kuma bukaci a sauya masa wata, sai dai Ibrahim ya ki ya yi hakan saboda a fadarsa cazar na yi a lokacin da ya saya.

Ya kara da cewa daga nan ne suka kama hannayensa suka tura shi cikin motarsu suka tafi da shi ofishinsu inda tun kafin a kulle shi wani jami’i ya fara da marinsa.

abdullahi-ibrahim-526x298

Ya ce daga nan ne sun bukaci ya tube rigarsa, ya kuma durkusa, suka fara dukansa har sai da ya ji ciwuka a bayansa, sannan suka dauko almakashi suka aske masa gashin kansa da gemunsa, suka bukaci ya tattara ya tura a aljihunsa.

Ya ce, bayan haka an bukaci ya rike kunnensa, sannan suka ce ya yi tsallen kwado ya fita daga ofishin, bayan da suka zaro kudaden aljihunsa suka zare 1500 a ciki.

Wata kungiyar masu kare hakkin dan adam a garin ta ce wannan ba shi ne karo na farko ba da wannan jami’i ke cin zarafin mutane, a dan haka za ta shigar da kara kotu game da al’amarin.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like