Zaman Tankiya Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila


4bkaf8de3c80d3gmug_800C450

 

A daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin Falesdinawa da yahudawan mamaya na Isra’ila, wani ministan Isra’lia ya shaida cewan Falesdinawa ba zasu iya hana zababen shugaban kasar Amurka, Donald Trump ba, sauya wa ofishin jakadancin Amurka a Isra’ila mazauni daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus ba.

Wadanan kalaman ministan hulda da kasashen yankin na Isra’ila, Tzachi Hanegbi  na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan kasashen duniya da suka halarci taron Paris kan zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa suka gargadi bangarorin biyu da su daina yin gaban kansa wajen daukar kowane irin mataki.

Da yake bayani ga manema labarai a birnin Kudus, Hanegbi ya Falesdina ba zasu iya komi ba, kuma komi ba zasu iya yi ba akan wannan matakin.

Mahukuntan Falesdinawa dai sun gargadi Mr Trump akan irin abunda zai iya biyo bayan daukan wannan matakin.

Zababen shugaban AMurka Donad Trump dai wanda zai yi rantsuwar kama aiki a ranar mai zuwa, yayi alkawari a yakin neman zabensa cewa, zai sauya wa ofishin jakadancin Amurka a Isra’ila mazauni daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus, matakin da ake ganin zai maida hannun agogo baya a yunkurin zamar da zamen lafiya tsakanin yahudawan mamayan na Isra’la da Falesdinu.

Gwamnatin Amurka mai barin gado ta bakin sakataren harkokin wajen ta John Kerry, tayi gargadi akan sake kunnowar wani sabon rikici a yankin gabas ta Tsakiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like