Zambiya: Zanga-zangar adawa da sakamakon zabe’


Yan sanda sun tsare mutane da dama a Lusaka babban birnin Zambiya. Tsare mutanen ya biyo bayan zanga-zangar ‘yan adawa na kin amince wa sakamakon zabe. 

Sakamakon zaben dai ya aiyana shugaba Edger Lungu a matsayin wanda ya lashe. Wannan lamarin ya jawo zaman zullumi a kasar da ake gani, mafi kwanciyar hankali a yankin.Fitar da sakamamkon zabe ke da wuya sai ‘yan adawa suka fantsama kan tituna, suna masu zargin gwamnati ta yi amfani da hukumar zabe don yin aringizon kuri’u. 

A kalla mutane 150 yan sanda suka tsare kawo yanzu, kamar yadda rahotanni daga Lusaka babban birnin kasar ta Zambiya suka bayyana. 

To shin ko menene hakanyake nufi ga makomar siyasar kasar ta Zambiya.”Lee Hobasanda shi ne daraktan kungiyar Transprancy Internationational a kasar Zambiya”Su dai yan adawa sun sanar da cewar tun fara yakin neman zabe gwamnati ta fara nuna alamunyin magudi, inda aka hana ‘yan adawa yin amfani da kakafen sadarwa yadda yakamata, haka kuma lokacin gudanar da zabe, akwai tsangwama da yawa ga masu goyon bayan ‘yan adawa musamman a yankunan da gwamnati ta fikarfi.”A halin yanzu sakamakon zaben ya nuna cewar kasar Zambiya ta kasu tsakanin banbancin kabiluda na magoya baya to ko “menene yafi damun mutanen kasar zambia duba da yadda zaben ya kasance? 

‘ Yan jaridu sun rawaito cewa:”To a halin yanzu dai suna cikin damuwa domin zaben ya kawo rarrrabuwar kai tsakanin yan’ kasar,jama’a sun fito sossai sun kada kuri’unsu,to amma an samu rashin juriyar adawa musamman daga bangaren jam’iyyar PF wadda har ta kai matakin makota ko ‘yanuwa suna gaba da juna irin duk saboda banbancin ra’ ayi.”Za dai a iya cewa akwai matukar bukatar ‘yan siyasa a kasar Zambiya su dau matakai na yafa wa wannan rikici ruwa, domin gudun kada a fada rikicin siyasa kamar yadda aka gani a wasu kasashen.

You may also like