Shekaru 20 Da Kafuwar Jihar Zamfara: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu?


abdulaziz-yari

 

 

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi gagarumin bikin cika shekaru ashirin da samun jihar.

Da yake masu iya magana na cewa ‘waiwaye adan tafiya’, idan ba a manta ba,

tun a shekara ta 1991 yankin Gusau da Birnin Kebi su kai ta gogoriyon raba su da Jihar Sokoto.

A shekara ta 1996, gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha , ya ce zai kara jihohi, inda nan take masu neman a kirkiro da Jihar Zamfara suka bazamana neman goyon bayan kananan hukumomin da su ke da bukatar zamowa cikin jihar ta Zamfara, karkashin jagorancin Alhaji Yusif Dan Hausa da A. A. Ladan, Alhaji Abu Zahara, Alhaji Sani Na Uma Bungudu da dai sauran mambobin kwamitin. Kuma bisa jajircewar sauran manyan jihar irin su Janar Ali Gusau da sauran su tabbatar da kafuwar jihar.

Ilimi shi ne gishirin rayuwa da ke gina al’umma, shin ta bangaren Ilimin wace nasara aka samu da kalubale?

Jihar Zamfara ta gaji Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Audu Gusau da ke Karamar Hukumar Talata Mafara da Kwalejin Koyan Aikin Gona da ke Bakura.

Daga nan sai jihar ta yi Kwalejin Horar da Malamai ta jihar a Maru da kuma Kwalejin Kiwon lafiya da ke Tsafe, da Makarantar Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma da ke Gusau.

Wadannan manyan makarantun idan aka auna su da sauran takwarorinsu na jihohi ba za su kai labari ba, sabo da halin ko in kula da ga gwamnatin jihar ta nuna musamman yadda wasu daga cikin makarantun ma haryanzu suna matsugunin su na wucin gadi ne. Sannan ayyukan da ke cikin makarantun kashi saba’in bisa dari sun samo shi ne daga hukumomin ba da dauki ga Ilimin na Gwamnatin Tarayya ba na jihar ba.

Batun makarantun firamare kuwa abin sai addu’a, don rashin ingantaccen albashi ga malamai da kuma ba da shi a kan lokaci, babbar matsala ace inda wasuke a cikinsu ma suke fadin cewa da ma a Jihar Sokoto suke saboda yadda albashin ma’aikatan jihar ya ninka nasu sau biyu.

Har ila yau, makarantun babu isasun ajujuwa, wadanda ake da su sun lalace musamman ma Makarantar Dan Turai da ke daura da Gidan Gwamnatin jihar, kai kace ba mutane a ke koyarwa ba.

Batun Asibitoci kuwa, suma sai a hankali matsalolinsu ya sa ma’aikatan kiwon lafiya kaurace ma jihar dan rashin ba su kulawa da su da majinyata. Babu magani a asibitoci, babu isasun ma’aikata. Tallafain abincin majinyata na asibitoci yau shekaru biyu kenan da daina badawa.

Kuma wani kalubale da jihar ke fuskanta shi ne na rashin Jami’a da Filin Jirgin Sama mallakarta.

Batun Tituna kuwa, Gwamna Yari ya yi kokarin hada kananan hukumomi da tituna na Gwamnatin Tarayya.

Batun ruwan sha kuwa, Baban birnin jihar Gusau ya lakume bilyoyin nairori amma har yanzu babu isasshen ruwa balle sauran kananan hukumomi.

Baki daya dai idan aka auna nasarorin da Jihar Zamfara ta samu daga lokacin da aka samar da al’umma za su yanke wa kansu hukuncin cewa, shin kwalliya ta biya kudin sabulu?


Like it? Share with your friends!

0

You may also like