Zamu Bawa Sauran Jam’iyyu Mamaki A Zaben 2019 – Sabuwar Jam’iyyar ADP



Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu a karkashin Jagorancin Muhammad Buhari da kuma Jam’iyyar adawa ta PDP data sha kayi a zabukan da suka gabata zasu sha mamaki a zabukan 2019 dake tafe.

Shugaban kasa da kasa na sabuwar Jam’iyyar ADP mai take (Action Democratic Party) Injiniya Yusuf Yabagi Sani shine ya bayyana haka a wani taro na cikin gida da suka yi a babban birnin tarayya dake Abuja.

Yace  Jam’iyyar ta ADP baza ta bata rawar ta da tsalle kamar yadda manyan Jam’iyyun kasar nan PDP da APC suka yi ba.

Yabagi yace Al’ummar Najeriya tun da dadewa sabuwar Jam’iyyar ADP suke jira kuma yanzu gashi sun fito, kuma zasu bayar da mamakin a zabukan dake tafe.

You may also like