Zamu Bijirewa Yunkurin Kara Farashin Kudin Mai – NUPENGKungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas ta Kasa NUPENG, ta soki yinkurin da majalisar dattawa take na karin kudin man fetur inda ta bayyana shirin a matsayin wani abun dariya. 

Da yake magana a birnin Legas, shugaban kungiyar reshen yanki kudu maso yammacin Najeriya, Tokunbo Korodo, yace shawarar kara kudin man  tazo a lokacin da bai dace ba, kuma rashin tausayine duba da halin matsin da yan kasa ke ciki.

Korodo yaja hankalin cewa ta yaya majalisar dattijai zata fara tunanin karin kudin mai yayin da yan Najeriya suke kokarin yaki da matsin tattalin arziki da suke fama dashi.

Yayi gargadin cewa idan har majalisar ba tayi watsi da kudirin ba to kuwa kungiyoyin kwadago zasu bijire masa. 

   ” Ta yaya majalisar dattijai zata fito da wannan kudirin a wannan lokacin da talakan Najeriya yake ciyar da kansa da kyar ” Korodo ya tambaya. 

“Farashin kayan abinci ya rubanya sau uku a kasuwa amma albashin ma’aikata bai karuba. ”

Kwamitin aiyuka na majalisar dattawa ne dai ya bada shawarar karin N5 akan kowace litar mai domin samar da kudi ga asusun kula da hanyoyi na kasa. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like