Shugaba Muhammad Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi guiwa a kasa ba sai ta ga Nijeriya ta sake rike matsayinta na kasar da ke fitar da abinci zuwa kasashen ketare a maimakon dogaro da abincin waje.
Buhari ya ce, baya kashi 90 cikin 100 na abincin da ake amfani da shi a Nijeriya, duk daga kasashen waje ake shi baiwa da shi amma ya ce, a halin yanzu abubuwa sun fara sauyawa ta yadda Nijeriya ta fara dogaro da kanta wajen samar da abinci.