Zamu Cigaba Da Fasa Bututun Mai Daga Ranar 30 Ga Watan YuniKwanaki kalilan bayan matasan Arewacin Najeriya suka yiwa yan kabilar Igbo barazana, kungiyar yan bindiga a Delta masu suna ‘New Delta Avengers’ sun alanta fito na fito da gwamnatin Najeriya da kamfanonin man fetur da ke yankin.

Kungiyar ya bindigan ta lashi takobin cewa zasu cigaba da kai hare-haren Bam a bututun mai da ke jihar Delta daga ranan 30 ga watan Yuni, 2017.

Kungiyar a wani jawabi ta bayyana cewa tana sanar da gwamnatin tarayya da kamfanonin mai da su shiryawa durkusar da fitar da man fetur da iskar Gas.

Kungiyar wadda tayi ikirarin cewa gamayyar tsoffin yan bindiga ne ta bayyana ta bakin kakakinta, CPL Oleum Bellum, cewa Duk wanda yayi kokarin sulhu kuma zai dandana gudarsa.

Sashen jawabin yace: “ Daga yankin fitar da mai a jihar Delta, mun hadu kuma mun yarje cewa zamu cigaba da kai hare-hare a bututun mai, zamu farfado da tsageranci kuma za mu bukaci fansa mai kyau da kuma jihar mu ta Delta. 

Za muyi wadannan  hare-hare masu zafi da kuma durkusar da kamfanin man da ke jihar Delta.”

You may also like