Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa majalisar za ta gaggauta dubawa tare da amince da kasafin kudin shekarar 2017 da zarar bangaren gwamnati ya gabatar da shi gaban majalisar.
Ya kuma tabbatar da cewa nan da kwanaki goma masu zuwa Shugaba Buhari zai gabatar wa majalisar da kasafin inda ya nuna cewa ya yi matukar gamsuwa bisa aikin da hukumomin gwamnati suka yi wajen tsara kasafin.