Zamu Gina Madatsun Ruwa 400 don Noman Rani Kafin 2019- BuhariShugaban Kasa, Muhammad Buhari ya tabbatar da cewa kafin shekarar 2019, gwamnatinsa za ta gina Madatsun ruwa 400 a duk fadin kasar nan don gudanar da noman rani.
Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar yaki da yunwa ta FCPN wanda aka yi a Abuja inda ya nuna cewa yawan ‘yan Nijeriya ya rubanya  a tsakanin shekaru 25 yana mai jaddada cewa a kan haka ne ya sa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen farfado da harkar noma da ma’adinai. 

Ya ce ta hanyar gina Madatsun ruwa ne, manoma za su iya yin noma sau uku a duk shekara.

You may also like