Zamu gina sabon gidan Yari a katsina  – Gwamnatin Tarayya


Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta gina sabon gidan yari a kan hanyar Jibiya dake cikin garin Katsina.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmimini Kabir Usman a lokacin bikin hawan barikin babbar sallah da ya gudana a tsohon gidan gwamnati da ke Katsina.

Kamar yadda ya ce, ministan kula da harkokin cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Danbazau mai ritaya ya ba da tabbacin hakan a lokacin da ya ziyarce shi inda ya ce aikin ginin sabon gidan yarin za a fara shi nd a kowane lokaci daga yanzu.

Gwamnan ya yi amfani da bikin wajen yaba ma jami’an tsaron a kan kokarinssu da kawar da barayin shanu a jihar wanda ya taimaka ma manoma wajen gudanar da ayyukan nomansu a wannan shekara.

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da ke kan iyakokin jihar da su sa ido a kan manyan motocin da ke fita da abinci maimakon su rika matsa ma wadanda ke daukar buhuna kadan a mashina.

Akan batun biyan albashi da mai martaba ya yi kuwa, Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnati na biyan kudaden albashi a kowane wata.

Gwamnan ya yi magana mai tsawo na cewa gwamnati mai ci yanzu ta dukufa wajen farfado da harkokin noma, ilimi, kiwon lafiya, samar da wadatattun ruwa da kuma harkokin tsaro.

Ya bukaci al’umma da su cigaba da yin adu’o’i domin samun zaman lafiya da kuma ganin Nijeriya ta farfado da tattalin arzikinta.

Tunda farko, mai martaba sarkin Katsinan Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci gwamnatin da ta rika biyan ma’aikata albashi a matakin jiha da kananan hukumomi a kan kari.

Kamar yadda yace, galibin jama’ar jihar ta dogara ne bisa albashin na wata-wata.

Ya bukaci al’umma da su yi hakuri kuma su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin fita cikin matsin tattalin arziki da ake ciki.

You may also like